Nigerian news All categories All tags
Babbar magana: Yansanda 13 ne suka taimaka ma yaran Dino Melaya da suka tsere daga Ofishin Yansanda

Babbar magana: Yansanda 13 ne suka taimaka ma yaran Dino Melaya da suka tsere daga Ofishin Yansanda

Rundunar Yansandan jihar Kogi ta tabbatar da rahoton tserewar wasu miyagun mutane guda 2 da suka tabbatar da cewar Sanata Dino Melaye ne ke basu makamai da kudi don su tayar da zauni tsaye.

Daily Trust ta ruwaito kwamishinan Yansandan jihar, Ali Janga ne ta bayyana haka a ranar Laraba 28 ga watan Maris, inda yace mutanen guda biyu da suka hada da Kabiru Seidu, inkiya Osama, da Nuhu Salisu inkiya Small, sun arce ne da misalin karfe 3:20 na dare, daga ofishin Yansanda na A dake Lokoja.

KU KARANTA: Ba zan je Kotu ba saboda gwamnan jiharmu ya shirya kashe ni – Inji wani Sanata Ba zan je Kotu ba saboda gwamnan jiharmu ya shirya kashe ni – Inji wani Sanata

Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya da yaran Melaye, akwai wasu mutane guda hudu da suka hada da Aliyu Isa, Adams Suleiman, Emmanuel Audu da Musa Muhammed, dukkaninsu sun tsere daga ofishin Yansandan.

Sai dai kwamishinan ya bada tabbacin a yanzu haka sun yi ram da yansandan guda 13 da ake zargi da taimaka ma yaran Melaye su tsere, inda yace tuni sun fara shan tambayoyi, don gani yadda aka haihu a ragaya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel