Nigerian news All categories All tags
Gwamnatin tarayya ta mayar da Tarihi a matsayin darasi mai zaman kansa a tsarin makarantu

Gwamnatin tarayya ta mayar da Tarihi a matsayin darasi mai zaman kansa a tsarin makarantu

- Gwamnatin tarayya ta bayar da umurnin cewa a mayar da Tarihi a matsayin darasi mai zaman kansa a tsarin makarantu

- Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana haka a wurin taron kaddamar da tarihi da kuma jagorancin malamai

- Yace, sabon tsarin anyi shi ne karawa dalibai fahimtar tarihi na yadda aka gina kasarsu

Gwamnatin tarayya ta bayar da umurnin cewa a mayar da Tarihi a matsayin darasi mai zaman kansa a tsarin makarantun Primary da Sakandare na kasar nan.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana haka, a ranar Talata, a wurin taron kaddamar da tarihi da kuma jagorancin malamai a birnin tarayya.

Yace, muhimmancin tarihin yadda aka gina kasa, asalin kasa, kaunar kasa, da kuma ci gaban dan Adam, duk zasu samu fahimtuwa ga daliban.

Gwamnatin tarayya ta mayar da Tarihi a matsayin darasi mai zaman kansa a tsarin makarantu

Gwamnatin tarayya ta mayar da Tarihi a matsayin darasi mai zaman kansa a tsarin makarantu

"Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta cigaba da shirinta canja tsarin ilimi- Tsarin Ministoci na (2016-2019), wanda ya kunshi abubuwa da dama. Wannan shiri ya samu amincewar hukumar ilimi ta kasa, a lokacin gudanar da taron majalisar ilimi, a watan Satumba na shekara ta 2016."

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Majalisar dinkin duniya ta zuba N4n domin ceto rayuka a Arewa maso gabas

Ministan yace, Cibiyar Nazarin Harkokin Ilimi ta Najeriya (NERDC), zata fitar da tsarin tarihi daga tsarin nazarin zamantakewa. Yace, sabon tsarin anyi shi ne karawa dalibai fahimtar tarihi na yadda aka gina kasarsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel