Nigerian news All categories All tags
2019: Ya kamata mu ba Atiku Abubakar dama – Dan majalisa ga PDP

2019: Ya kamata mu ba Atiku Abubakar dama – Dan majalisa ga PDP

Dan majalisar jihar Lagas, Mista Dipo Olorunrinu ya bukaci jam’iyyar PDP da ta ba tsohon mataimanin shugaban kasa Atiku Abubakar daman tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019.

Olorunrinu dan majalisa daya tilo daga jam’iyyar PDP a majalisar dokokin jihar Lagas ya bada wannan shawara ne a yayi zantawa da kamfanin dillancin labarai a ranar Laraba.

Dan majalisan ya bayyana cewa Atiku na da kwarewa tsawon shekaru sannan kuma cewa ya kansace mara nuna kabilanci gashi kuma dan siyasa mai kishin kasa.

Ya bayyan cewa wasu mutane basu son Atiku ne saboda wani ra’ayi na son zuciyarsu.

2019: Ya kamata mu ba Atiku Abubakar dama – Dan majalisa ga PDP

2019: Ya kamata mu ba Atiku Abubakar dama – Dan majalisa ga PDP

Kan yawan mutane dake neman kujerar shugabancin kasa a PDP, dan majalisan ya bukaci da su marawa dan takara mafi inganci baya wanda zai iya kai jam’iyyar ga nasara a 2019.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata a hukunta Danjuma - Inji kungiyar shari’a

Kan batun hakuri da jam’iyyar ta bayar Olorunrinu yace hakan ya nuna cewa jam’iyyar ta na tausayi sannan kuma a shirye take ta sake inganta kasar Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel