Kiwon lafiya: Bakuwar cuta mai kashe yara ta shigo cikin Garin Kano

Kiwon lafiya: Bakuwar cuta mai kashe yara ta shigo cikin Garin Kano

- A cikin makonnin nan ne wata cuta ta shiga Kauyukan Jihar Kano

- Wannan cuta mai kama da zazzabi tayi sanadiyyar mutuwar yara

- Gwamnatin Jihar Kano ta fara daukan matakin da ya dace a yanzu

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa wata bakuwar cuta ta shiga Unguwar Dungurawa a Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano inda tayi sanadiyyar kashe mutane 10.

Kamar yadda labari ya zo mana, wannan cuta da ta shigo cikin gari mako biyu da su ka wuce tana kashe kananan yara ne. Wani Bawan Allah mai suna Sulaiman Musa Tafida ya rasa yaran sa uku bayan markewar cutar.

Wanda ya rasa iyalin na sa yace da farko ya dauka cutar masassara ce ta kama yaran na sa. Daga cikin alamun wannan cuta akwai zazzabi da amai da guduwa. Cikin wanda ya kamu da cutar yana barkewa da mugun zafi.

Yanzu haka har yanzu wasu marasa lafiya su na kwance a asibiti a Garin Bichi. Hukuma dai ta aika Malaman asibiti da magugunan rigakafi zuwa Yankin da cutar ta barke gudun yaduwa bayan Jama’a sun kai kukan su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel