Nigerian news All categories All tags
Hukumar Hisbah na Kano ta kama almajirai 105 da suke keta dokar hana bara

Hukumar Hisbah na Kano ta kama almajirai 105 da suke keta dokar hana bara

Hukumar Hisbah ta jihar Kano tace ta kama almajirai 105 a jihar a watan Fabrairu kan zargin keta dokar hana bara a unguwanni.

Malam Dahiru Nuhu, jami’in dake kula da sashin hana bara, ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Laraba.

Nuhu ya bayyana cewa 35 cikin wadanda aka kama a yayin farmakin sun kasance yara yayinda 60 suka kasance manya.

Ya bayyana cewa anyi kamun ne a yankunan dake kewaye da filayen ajiye motoci da asibitoci.

A cewar jami’an Hisbah, an saki wasu daga cikin wadanda aka kama wanda suka kasance sabbin shiga a harkan yayinda aka gurfanar da tsoffin hannu a gaban kotu.

Hukumar Hisbah na Kano ta kama almajirai 105 da suke keta dokar hana bara

Hukumar Hisbah na Kano ta kama almajirai 105 da suke keta dokar hana bara

Ya bayyana cewa wasu bayin Allah sun dawo da wasu almajirai 10 da suka bata yan shekaru bakwai da 10 inda aka mayar da su makarantun su.

Nuhu ya bukaci mutane da su bar sana’ar almajiranci sannan su koyi ayyuka masu amfani da hannayensu domin tafiyar da al’amuransu na yau da kullun.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Majalisar dinkin duniya ta zuba N4n domin ceto rayuka a Arewa maso gabas

Kamar yadda kuka sani, rahotanni sun kawo cewa duk wanda ya saba ma dokar kiwo a jihar toh zai fuskanci daurin watanni uku a gidan yari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel