Nigerian news All categories All tags
APC ta saduda bayan Shugaba Buhari yace ba ya na’am da karawa Oyegun wa’adi

APC ta saduda bayan Shugaba Buhari yace ba ya na’am da karawa Oyegun wa’adi

- APC za ta dauki mataki bayan jawabin Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Shugaban kasar yace doka ba ta bada damar a karawa John Oyegun wa’adi ba

- Dalilin haka Majalisar zartawa na Jam’iyyar tayi wani zaman gaggawa a boye

Dazu nan mu ke jin cewa APC mai mulki ta shirya gudanar da gangamin ta. APC za ta sa ranar da za tayi babban taron ta ne inda za ta zabi sababbin Shugabannin Jam’iyyar bayan Shugaba Buhari yace bai dace a karawa Shugabannin wa’adi ba.

APC ta saduda bayan Shugaba Buhari yace ba ya na’am da karawa Oyegun wa’adi

Shugaba Buhari ya ba manyan APC mamaki bayan ya nemi a sauke su Oyegun

Majalisar zartarwa watau NEC ta Jam’iyyar tayi wani taro a boye inda ta dauki shawarar Shugaban kasar kamar yayda mu ka samu labari daga daily Trust. A ka’ida dai wa’adin shugabannin zai kare ne nan da watanni 3 masu zuwa.

KU KARANTA: Buhari yayi maganin rikici a APC inji Shehu Sani

Gwamnonin APC ba su ji dadin matakin da Shugaban kasa Buhari ya dauka ba a jiya. Yanzu dai Jam’iyyar za ta zabi shugabannin da za su ja ragamar al'amura domin a gudunar da zaben fitar da gwani a daf da karshen shekarar nan.

Manyan Jam’iyyar irin su Gwamnonin Jihohi da Ministoci da su ka nemi a karawa Oyegun matsayi sun yi haka ne saboda Jam’iyyar ta hana wasu ‘Yan Majalisa tikiti a 2019. Shi dai Bola Tinubu da mutanen sa sun ji dadin abin da ya faru a taron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel