Nigerian news All categories All tags
Ku kare kawunanku ba tare da daukar makamai ba - Ortom

Ku kare kawunanku ba tare da daukar makamai ba - Ortom

- Gwamnan jihar Binuwai, Sam Ortom, yace ‘yan Najeriya su tashi tsaye don su kare kansu ba tare da sun rike makami ba

- Gwamnan yace, mutane zasu iya amfani da sanda sun kwace makaman ‘yan ta’adda, bayana an tina da cewa ya taba kwace makaman ‘yan fashi da makami a baya

- Yace harkar tsaro ba abunda za’a barwa jami’an tsaro bane kadai, amma abu ne wanda za’a hada hannu da duka jama’ar Najeriya

Gwamnan jihar Binuwai, Sam Ortom, yace ‘yan Najeriya su tashi tsaye don su kare kansu ba tare da sun rike makami ba.

Gwamnan yace, mutane zasu iya amfani da sanda su kwace makaman ‘yan ta’adda, bayana tinawa da cewa ya taba kwace makaman ‘yan fashi rike da bindiga kirar AK-47, a baya.

Yace harkar tsaro ba abunda za’a barwa jami’an tsaro bane kadai, amma abu ne wanda za’a hada hannu da duka jama’ar Najeriya.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya zanta da manema labarai na gidan gwamnati, a ranar Talata bayan sunyi ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake birnin tarayya.

Ku kare kawunanku ba tare da daukar makamai ba - Ortom

Ku kare kawunanku ba tare da daukar makamai ba - Ortom

Lokacin da ya maida murtani akan kiran da tsohon Ministan Tsaro, Theophilus Danjuma, yayi, inda yace, mutane su kare kannsu, Ortom, yace anyiwa maganara danjuma fasara ta daban.

Yace Danjuma, baice kowa ya dauki makami ba, kawai yace mutane su kare kansu, kuma gaskiya ne, kare kai shine abu na farko a ka’idar rayuwa.

Yace, fadawa shugaban kasa maganar sansanin ‘yan gudun hijira takwas dake akwai a jihar, wanda ke dauke da mutane 175,000, wadanda suka nuna bukatarsu ta komawa gidajensu.

Ya kuma bayyana cewa shugaban kasar, ya tabbatar masa da daukar mataki akan korafe-korafen da aka gabatar masa na ‘yan gudun hijira da kuma sauran matsaloli.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Majalisar dinkin duniya ta zuba N4n domin ceto rayuka a Arewa maso gabas

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel