Hukumar NEMA ta sake yakito 'yan Najeriya 149 daga kasar Libya

Hukumar NEMA ta sake yakito 'yan Najeriya 149 daga kasar Libya

Rahotanni da sanadin jaridar Vanguard sun bayyana cewa, hukumar agaji ta kasa watau NEMA (National Emergency Management Agency), tare da hadin gwiwar cibiyar haure ta duniya, sun sake yakito 'yan Najeriya 149 daga kasar Libya.

Manema labarai sun ruwaito cewa, bakin na haure sun sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake jihar Legas da misalin karfe 10.49 na daren ranar Alhamis din da ta gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, bakin hauren sun hadar da maza 107, mata 37 da kuma kananan yara hudu da na goye guda daya.

Hukumar NEMA ta sake yakito 'yan Najeriya 149 daga kasar Libya
Hukumar NEMA ta sake yakito 'yan Najeriya 149 daga kasar Libya

Shugaban cibiyar haure ta kasa, Mista Abraham Tamrat, shine ya mika bakin hauren ga shugaban hukumar agaji reshen yankin Kudu maso Yammacin kasar nan, Alhaji Yakubu Suleiman.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta bukaci a sako dalibar Dapchi ta karshe dake hannun 'yan ta'adda

Alhaji Sulaiman ya yiwa cibiyar ta IOM godiya da yaso 'yan Najeriya dake cikin kangin kakanikayi wajen yunkurin haurewa zuwa kasashen Turai daga kasar Libya.

Ya kuma shawarci bakin haure akan su kauracewa jefa kan su cikin wahala tare da gargadin su da cewa garin neman gira akan rasa idanu.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wata mahaifiya ta bayar da diyar ta jinginar bashin N100 da ya yi ma ta katutu a jihar Ebonyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel