Kungiyar JNI ta yabawa gwamnati akan 'yan matan Dapchi

Kungiyar JNI ta yabawa gwamnati akan 'yan matan Dapchi

Kungiyar Jama'atu Nasril Islam a ranar Larabar da ta gabata ta yabawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a sakamakon sauke nauyin da rataya a wuyan ta wajen kwazo na ceto 'yan Matan Dapchi.

Babban sakataren kungiyar, Dakta Khalid Abubakar, shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na kasa a garin Kaduna, inda ya ce tabbas gwamnatin kasar nan ta cancanci yabo.

Kungiyar ta kuma yabawa iyaye, hukumomin tsaro musamman jami'an DSS da sauran masu ruwa da tsaki dangane da wannan labari mai sanya baka har kunne.

Kungiyar JNI ta yabawa gwamnati akan 'yan matan Dapchi
Kungiyar JNI ta yabawa gwamnati akan 'yan matan Dapchi

Babban sakataren ya nemi gwamnati akan ta kara jajircewa tare da hobbasa wajen ceto sauran 'yan Matan Chibok da kuma dukkan wanda ya ke neman kubuta daga ta'addanci a fadin kasar nan.

KARANTA KUMA: Hukumar Sojin kasa ta karyata kungiyar Amnesty International akan 'yan Matan Dapchi

Kungiyar ta kuma nemi gwamnatin tarayya akan ta baza wadatattun jami'an tsaro a makarantu wanda hakan ya kasance daya daga cikin nauye-nauyen gwamnati na tabbatar da kariya da rayuwar al'ummar ta da kuma dukiya.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar JAMB ta rike sakamakon jarrabawar wasu dalibai ma su neman shiga jami'o'i a jarrabawar bana ta shekarar 2018 domin tsananta bincike akan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel