Makiyaya sun kashe sarkin gargijiya, uwargidanshi da wasu mutane 9

Makiyaya sun kashe sarkin gargijiya, uwargidanshi da wasu mutane 9

Akalla mutane 9 sun rasa rayukansun a hannun makiyaya wanda ya kunshi sarki Onu Agbenema, Musa Edibo; da uwargidansa, kuma sun kona gidaje a kauyukan Agbenema, Aj’Ichekpa, Opada da Iyade, ranan Litinin.

Garin Agbenema na karamar hukumar Omala na jihar Kogi.

Maharan wadanda ke dauke da muggan makamai sun boye cikin daji ne inda suka kai hare-haren.

Game da cewar, makiyaya su kan bankawa gidajen mutane wuta sannan su kashe mutanen da ke kokarin tsirata da rayukansu.

Daga cikin wadanda aka kona musu gidaje shine tsohon shugaban karamar hukumar, Adofu Stephen, da kuma na iyayensa.

Makiyaya sun kashe sarkin gargijiya, uwargidanshi da wasu mutane 9
Makiyaya sun kashe sarkin gargijiya, uwargidanshi da wasu mutane 9

Mazaunan sun kara da cewa sojin da aka tura dakile rikicin sun ki kawo musu agaji yayinda suka bukata.

KU KARANTA: Sai Buhari ya fara canza kansa da na mukarrabansa kafin aga canji a kasar – Bashir Tofa

“Mun yi mamaki lokacin da muka tuntubi sojin da aka ajiye a Abejukolo domin agaji.”

“Sun yi banza da mu, kana sun hana mu karasawa wajen domin taimakawa mutanensu.”

“Sun babbaka garin Ojuwi, Ajomayeigbi, Iyade, Agbenema da Opada.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuhttps://twitter.com/naijcomhausantube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel