Bayan ya buge wata da babur, jami’an SARS ya kasha dan kasuwa ba gaira ba dalili

Bayan ya buge wata da babur, jami’an SARS ya kasha dan kasuwa ba gaira ba dalili

Wani jami’in hukumar SARS da yammacin ranan Talata ya hallaka dan kasuwan dabbobi mai suna Ibrahim Ali, wanda akafi sani da Mbaba, a kauyen Ganaja, garin Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

An samu labarin cewa wannan rikicin ya barke ne yayinda wasu matasa suka kwace babur din jami’in SARS bayan ya buge wata yarinya.

Idanuwan shaida da ke wurin sun bukaci dan sandan ya kai yarinyan asibiti amma ya ki, sai ya fara kiran abokan aikinsa.

Wannan al’amari ya munana yayinda abokan aikinsa suka karaso. Matasan suka jaddada cewa lallai fa sai an kai yarinyan asibiti. Da mujadala yayi nisa, daya daga cikin jami’an SARS ya fito da bindiga kawai ya fara harbi sama domin tsorata mutane, amma sai harsashi ya sami Mbaba yana gaban shagonsa.

Bayan ya buge wata da babur, jami’an SARS ya kasha dan kasuwa ba gaira ba dalili
Bayan ya buge wata da babur, jami’an SARS ya kasha dan kasuwa ba gaira ba dalili

Wannan abu ya fusata mazauna garin wanda ya jawo hayaniya. Daga karshe suka dauki gawan shi suka kawai hedkwatansu.

KU KARANTA: Guguwar Buhari baza ta yi aiki ba zaben 2019 – Gaddama

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Aya Williams, wanda ya tabbatar da wannan kisa yace an kaddamar da bincike cikin wannan al’amari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel