Yakubu Dogara yace kwanan nan nakasassu zasu dara a kasar nan

Yakubu Dogara yace kwanan nan nakasassu zasu dara a kasar nan

- Majalisar wakilai sun yi zama kan yadda zasu taimakawa gajiyayyu

- Yakubu Dogara yace lallai zasu yi dokar kare hakkin marasa galihu

- An maida marasa galihu da nakasassu almajirai a kasar nan

Yakubu Dogara yace kwanan nan nakasassu zasu dara a kasar nan
Yakubu Dogara yace kwanan nan nakasassu zasu dara a kasar nan

Yakubu Dogara ya lashi takobin samar wa da nakasassu dokar da zata kare su, kuma ta kumanta su, da ma sama musu mafita ba bara ba.

Wannan na zuwa ne yayi da yake karbar wakilai Kpankpando Foundation For Persons With Disabilities wadanda suka kai masa ziyara a Abuja a yau Laraba. Ita dai kungiyar tana da muradun kare hakkin guragu da makafi da sauran nakasassu ne.

DUBA WANNAN: Ina iyaka kokarina wajen sama muku aikin yi

Kakakin majalisar yace majalisar wakilai na aiki kan sabuwar dokar kare hakkin gajiyayyu da nakasassu, kuma nan bada dadewa ba za'a gani a kasa.

A Najeriya dai, ana wulakanta nakasassu, inda babu abun da zasu iya yi banda bara da garararmba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel