An kama bindigu a motar kamfen din wani dan takarar majalisar a jam'iyyar APC

An kama bindigu a motar kamfen din wani dan takarar majalisar a jam'iyyar APC

- A yayinda shekar 2019 ke kara karatowa, 'yan siyasa na kara haukacewa wajen neman takara ta kowacce hanya

- Al'amuran siyasa a jihar Kogi sun dade da daukan zafi, musamman rashin jituwa dake tsakanin gwamnan jihar, Yahaya Bello, da Sanata Dino Melaye

- Ba a ji ta bakin dan takarar majalisar da aka kama motar yakin neman zabensa dauke da bindigun ba

An kama motar ne da wani matashi da ya yi ikirarin shi kani ne wurin dan takarar majalisar a jihar Kogi.

Dakarun soji ne su ka kama motar bayan motar ta lalace a hanya.

Da dakarun sojin ke yi masa tambayoyi, matashin ya ce, ya je dauko mai gyara ne sai kawai ya dawo ya ga jami'an tsaro sun kewaye motar. Ya kara da cewar dan acabar da ya dauko shi ya ba shi shawara ya gudu amma ya ki.

An kama bindigu a motar kamfen din wani dan takarar majalisar a jam'iyyar APC

An kama bindigu a motar kamfen din wani dan takarar majalisar a jam'iyyar APC

Matashin ya ce ya je karbo kudi wurin dan uwansa domin gyara motar amma sai ya dawo ya tarar da jami'an tsaro a wurin.

DUBA WANNAN: Ihu bayan hari: Trump ya bayyana dalilin cire sakataren wajen Amurka

Matashin ya ce bindigu biyu ne kawai a motar. Sai dai bai ambaci ko waye keda mallakinsu ba.

Motar, kirar Toyota, na like da hoton dan takarar majalisa, Aduga.

Ya zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin dan takarar majalisar ba.

Ku kalli faifan bidiyon matashin a kasa, yayin da dakarun ke yi masa tambayoyi:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel