Zaben 2019: Ba za mu amince Majalisa tayi amfani da karfin iko wajen canja jadawalin zabe ba - Sanatocin APC

Zaben 2019: Ba za mu amince Majalisa tayi amfani da karfin iko wajen canja jadawalin zabe ba - Sanatocin APC

- Sanatocin jam'iyyar APC sun dau alwashin kin amincewa da duk wata yunkuri da Majalisar Dattawa za tayi wajen canja jadawalin zaben 2019

- Sanata Adamu ya ce idan kayi zabe sau biyu, za'a fi samun saukin samar da tsaro sakamakon gudanar da zaben cikin makonni uku

- Ya kuma yi kira ga sauran abokan aikin sa da su hakura su bar jadawalin zabe yadda yake saboda ba alheri bane ga al'umma

Sanata Ali Ndume da ke wakiltan yankin kudancin Borno ya bayyana cewa shi da sauran Sanatocin jam'iyyar APC ba za su amince da duk wata hanya da Majalisar za tayi amfani dashi wajen yin kwaskwarima ga jadawalin zabe ba tare da amincewar Buhari ba kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

Canja jadawalin zabe 2019: Ba za mu amince Majalisa tayi amfani da karfin iko wajen tursasa Buhari ba - Sanatocin APC

Canja jadawalin zabe 2019: Ba za mu amince Majalisa tayi amfani da karfin iko wajen tursasa Buhari ba - Sanatocin APC

A cewar Sanata Ndume: "Idan sukayi wata yunkurin yiwa shugaban kasa kewaye kan batun, zamu taka musu birki. A kalla mun haura 43 a Majalisar kuma wasu Sanatocin ma sun bayyana goyon bayan su gare mu. Muna kira ga sauran abokan aikin mu su hakura da batun don ba alheri bane ga al'umma."

KU KARANTA: Yadda wata 'yar aiki mai shekaru 11 ta kashe 'dan masu gida babu gyara babu dalili

"Gudanar da zaben sau biyu, za'a fi samun saukin samar da tsaro sakamakon gudanar da zaben cikin makonni uku."

Majiyar Legit.ng kuma ta gano cewa shima Sanata Abdullahi Adamu ya dau alwashin ganin cewa Majalisar bata sauya jadawalin zaben ba.

Adamu ya ce: "Bana son yin fallasa a kafafen yadda labarai. Ina gudanar da abubuwa ne idan lokacin su ya yi. Duk wanda suke yunkurin yiwa jadawalin kwaskwarima sun san akwai sauran magana.

"Ba su ga komai ba yanzu, ku fada musu cewa ba'a kamalla yiwa jadawalin zaben kwaskwarima ba. Insha Allahu, na yi alkawari kuma ba zan ci amanar jam'iyyar ta ba."

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa Hukumar zabe mai zaman kanta INEC za tayi biayaya ga sabon jadawalin zaben idan har yan majalisar sukayi nasarar tabbatar da kudirin a matsayin doka wata 6 kafin babban zaben na 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel