Gwamna Lalong ya sallami shugaban karamar hukuma kan kashe-kashe

Gwamna Lalong ya sallami shugaban karamar hukuma kan kashe-kashe

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya fatattaki shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Bokkos, Simon Angol, a sakamakon gazawar sa na kawo karshen kashe-kashe da ya yi kamari a yankin sa.

Bayan daukar shawarwari na shugaban majalisar dokoki ta jihar, gwamnan ya aika da takardar sallama inda kakakin majalisar Peter Azi ya karance ta a zaman majalisar da aka gudanar na talata ga sauran 'yan majalisu.

Gwamnan ya sanya laifi kan shugaban karamar hukumar wajen gazawar sa na samar da mafita tare da kawo karshen tashin-tashina a yankin sa da suke ta afkuwa kusan mako guda.

Gwamnan jihar Filato; Simon Lalong

Gwamnan jihar Filato; Simon Lalong

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, wasikar gwamnan ta kuma nemi Mr Tamai Simon a matsayin sabon shugaba da zai maye gurbin kujera ta shugabancin karamar hukumar.

KARANTA KUMA: Yaki da rashawa: Sai Buhari ya damke Obasanjo za mu san dagaske yake - Kalu

Rahotanni sun bayyana cewa, rikici a karamar hukumar Bokkos ya afku a tsakanin ranar Larabar makon da ya gabata zuwa safiyar ranar Lahadi, inda kimanin rayuka 26 da tarin dukiya suka salwanta.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, domin tabbatar da gaskiya da muhimmancin yaki da rashawa, tsohon gwamnan jihar Abia Orji Uzor Kalu, ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya damke tsohon shugaban kasa Obasanjo bisa wasu laifukan rashawa da suka afku a lokacin gwamnatin sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel