Angela Merkel ta Jamus taci zabe a karo na biyar, ga abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da ita

Angela Merkel ta Jamus taci zabe a karo na biyar, ga abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da ita

- Angela Dorothea Kasner, wadda akafi sani da, Angela Merkel, an haifeta a Hamburg, Yammacin Jamus, 17 ga watan Yuli, shekarar 1954

- Angela Merkel macece mafi girma a duniya, shugabar kasar dake jagorancin tattalin Arzikin Turai

- Kamar sau 10, masu hasashe suka sanyata a matsayin ‘‘mace mafi karfi a duniya’’

Angela Merkel ta Jamus taci zabe a karo na biyar, ga abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da ita

Angela Merkel ta Jamus taci zabe a karo na biyar, ga abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da ita

Angela Dorothea Kasner, wadda akafi sani da Angela Merkel, an haifeta a Hamburg, Yammacin Jamus, 17 ga watan Yuli shekarar 1954.

A matsayin malamar kimiyya mai digiri uku, Merkel ta shiga siyasa bayan faduwar Berlin a shekarar 1989. Data kara sama zuwa matsayin shugabar jam’iyyar Christian Democratic Union, Merkel ta zama shugaba ta farko a Jamus, kuma daya daga cikin kasashe manya-manya na Tarayyar Turai, bayan zaben shekarar 2005.

Angela Merkel, itace mace mafi girman kujerar siyasa a duniya, shugabar kasar dake jagorancin tattalin Arzikin Turai. Likita ce mai son wasan kwallo wadda kuma aka bada rahoton cewa tana tsoron karnuka.

DUBA WANNAN: EFCC na neman N12B a hannun Modu Sherif

A yau da ta lashe zabe a karo na biyar a jere, bari mu karanta wasu abubuwa da ba dayawa suka sansu ba game da ita ba.

1. Kamar sau 10 masu hasashe suka sanyata a matsayin “mace mafi girma a duniya”, sau biyu kuma an sata a matsayi na biyu bayan Vladimir Putin a cikin jerin sunayen da masu hasashe keyi a matsayin ‘Mace Mafi Girma a Duniya’.

2. A shekarar 2015, an kirata da matsayin matumin shekara a wata mujalla ta Time, a bayan mujallar an kirata da matsayin ‘Chancellor of Free World’ ma’ana Jagora ta ‘Yanci ta Duniya. Tun daga wannan lokaci, an kwatanta ta a matsayin ‘Jagora ta ‘Yanci ta Duniya’.

3. Merkel, daga lokacin da take jagorancin jam’iyyar adawa, tayi jawabi kan abokantakar tsakanin Jamus da Amurka, kuma ta kasance da kyakkyawan Abokantaka tsakaninta da shugaban kasar Amruka Goerge W. Bush dama Barrack Obama.

4. Merkel itace mafi tsawon-zama a shugabancin gwamnati a tarihin Tarayyar Turai, a cikin watan Maris na 2014.

5. Magoya baya a Jamus suna kiranta da Mutti, ma’ana “Mommy”

6. Tana da takardar Digiri a fannin lissafi da Likintanci a fannin kimiyya, kuma wasu sun ce nasararta a matsayin siyasa ta fito ne daga kimiyyarta, da nazarin tsarin bincikenta. Ta cigaba dayin aiki a matsayin masaniyar kimiyya, a matsayinta kawai na mace a bangaren ilimin kimiyya a Cibiyar Kimiyya ta Gabashin Jamus.

7. Da farko dai, Merkel taso ta zama Malamar koyar da Harshen Rasha da Ilimin Lissafi. A karshe, ta zama likita kuma tanada Digiri daga Jami’ar Leipzig. A cikin takaddamarta, Merkel ta bincika tasiri na hadin gwiwar sararin samaniya a cikin magunguna a kafofin watsa labarai na Bimolecular.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel