Hukumar INEC ta bakado wata cibiyar rajista ta boge a jihar Neja

Hukumar INEC ta bakado wata cibiyar rajista ta boge a jihar Neja

Hukumar zabe ta kasa wato INEC reshen jihar Neja, ta bayyana cewa ta bankado wata cibiyar boge ta rajistar katin zabe a garin Zungeru dake karamar hukumar Wushishi ta jihar.

Shugaban reshe, Farfesa Sam Egwu, shine ya bayyana hakan ga manema labarai na jaridar Daily Trust a ranar Talatar da ta gabata da cewa, hukumar 'yan sanda ce tayi nasarar damko masu hannu cikin wannan ta'asa dauke da katukan na zabe.

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmoud Yakubu

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmoud Yakubu

Farfesan a birnin Minna ya ci gaba da cewa, mafi akasarin masu afkawa mazambatan leburori ne dake fafutikar samun katin zabe cikin sauki domin kada kuri'un su a zaben kasa mai gabatowa.

Legit.ng ta fahimci cewa, mazambata su kan karbi tukwici ga duk wanda ya afkawa tarkon su na neman rajista tare da samun katin zabe.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya bayyana dalilin watsi da dokar sauya fasalin zabe

Shugaban ya kara da cewa, hukumar ta sake kafa wasu sabbin cibiyoyi goma a jihar domin baiwa al'umma damar samun rajista da mallakar katin zabe cikin sauki.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani sabon bincike ya tabbatar da nasabar wata cutar kwakwalwa zuwa ga yawan baccin rana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel