Ihu bayan hari: Trump ya bayyana dalilin cire sakataren wajen Amurka

Ihu bayan hari: Trump ya bayyana dalilin cire sakataren wajen Amurka

- A jiya ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cire sakataren wajen Amurka Rex Tillerson

- Da ma dai ba a ga maciji tsakanin Trum da tsohon sakataren wajen Amurka Rex Tillerson

- Trump ya ce, cire Tillerson ba ta da alaka da rashin shirin dake tsakaninsu

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ba ya cire sakataren wajen Amurka, Rex Tillerson, ba ne saboda sabanin fahimta dake tsakaninsu a kan batun mayar da ofishin jakadancin Amurka Jerusalem ba ko sabanin fahimta a kan alakar Amurka da Rasha ba.

Wasu kalaman cin mutunci da Tillerson ya yi a kan Trump shekarar da ta gabata da kuma yawaitar banbancin ra'ayin dake tsakaninsu ne ya jawo Trump ya cire Tillerson ranar Talata.

Ihu bayan hari: Trump ya bayyana dalilin cire sakataren wajen Amurka

Trump da Tillerson

'Yan jam'iyyar Republican ta shugaba Trump sun ce shugaban ya gaji da daukan shawarar da su ke ba shi a kan bukatar ya sassauta yawan nadi da sauke mukamai a gwamnatinsa, domin bai shawarci jam'iyyar ba kafin cire Tillerson.

Wani dan jam'iyyar ya bayyana cewar Trump ya fi kaunar yin abinda yake so kuma ta hanyar da ya ke so tare da bayyana cewar halayyar Trump kan iya jawowa jam'iyyar rasa rinjaye a zabukan tsakiyar zango.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya zata biya kowanne sansani dala $2,500 a matsayin kudin fansar 'yan Najeriya a Libiya

Hatta shi kansa Tillerson ya yi matukar mamaki bayan da wani daga cikin hadimansa da su ke rangadin kasashen Afrika tare ya nuna masa sakon cire shi a shafin Tuwita na Trump.

Cire Tillerson ba shine karo na farko da Trump ke sauke manyan mukamai a Amurka ba. Ko a ranar Litinin saida ya sa aka fitar da wani mataimakinsa na musamman, McEntee, daga fadar mulkin kasar Amurka bayan ya cire shi daga mukaminsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel