Kisan da Makiyaya ke yi zai iya haddasa yaki - Gwamna Umahi

Kisan da Makiyaya ke yi zai iya haddasa yaki - Gwamna Umahi

- Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya mayar da murtani ga rikici tsakanin Manoma da Makiyaya a garin Enyanwu Igwe Igbeagu

- Gwamnan ya umurci Makiyayan dasu gaggauta barin garin na Enyanwu Igwe Igbeadu

- Yace bazai iya sa ido ya bar kisa irin wanda kisar da akeyi a jihar Binuwai ya faru a jihar shi ba

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, yayi gargadin cewa artabon Makiyaya da Manoma zai iya haddasa Yaki a Najeriya, idan ba’ayi a hankali ba.

Umahi yayi jawabi ne a wani taro a ranar Talata, 14 ga watan Maris, a lokacin dayake mayar da martini kan wani hari da ya faru a ranar Litinin, lokacin da makiyaya suka kaima Manoma hari a kauyen Enyanwu Igwe Igbeagu, a karamar hukumar Izzi.

Kisan da Makiyaya keyi zai iya haddasa yaki - Gwamna Umahi

Kisan da Makiyaya keyi zai iya haddasa yaki - Gwamna Umahi

Jaridar Premium Times ta bayyan cewa, shuwagabannin Makiyaya na Kudu maso Gabas da na kudu maso kudancin jihar, jama’ar kauyen da abun ya shafa, da kuma shuwagabannin hukumomin tsaro na jihar sun halarci taron.

KU KARANTA: An kama wata mata a Katsina bisa zargin kashe diyar kishiyarta

Gwamnan ya umurci Makiyayan dake zama a yankunan da abun ya shafa dasu gaggauta barin yankunan, don gudun cigaba da tashin hankalin, don kuma gwamnati ta samu damar shiga cikin al’amarin ta kwantar wa mutanen da hankali.

Bayan haka, Legit.ng ta kawo muku rahoton inda wasu Makiyaya suka kashe mutane 23 a wani sabon hari da aka kai a kauyen Dundu, Miango a karamar hukumar Bassa, Plateau.

Shugaban matasan Miango, Auta Danjuma, yace harin an kaishi ne a daren Litinin, 12 ga watan Maris. Yace yawancin mutanen da aka kashe matane da yara wasu kuma anji masu raunuka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel