Yansanda sun kama mutane shida dangane da jifar da aka yiwa gwamnan jihar Neja

Yansanda sun kama mutane shida dangane da jifar da aka yiwa gwamnan jihar Neja

- Jami'ian yansandan jihar Neja sun kama mutane shida dangane da jifar da aka yiwa gwamna Sani Bello

- Yansanda sun fara bincike dan gano mutanen da suka dauki nauyin jifar da aka yiwa gwamnan Neja a makon da ta gabata

Rundunar ‘yansandan jihar Neja sun kama mutane shida da ake zargi suna da hannu a jifa da duwatsu da aka a yiwa gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello a garin Bida a makon da ya gabata.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Neja, Mista Dibal Yakadi, ya bayyana haka a ranar Laraba a birnin Minna.

Yansanda sun kama mutane shida dangane da jifar da aka yiwa gwamnan jihar Neja

Yansanda sun kama mutane shida dangane da jifar da aka yiwa gwamnan jihar Neja

A ranar 8 ga watan Mayu ne wasu gungun matasa suka yiwa gwamnan jihar Neja ruwan duwatsu a lokacin da yaje jajantawa mutanen karamar hukumar Bida da ibtilai’n gobara ya afkawa babban kasuwar garin.

KU KARANTA : Soja ta kashe wata mata a garin Aba

Gwamna Sani Bello, ya yiwa ‘yan kasuwar kyautar naira miliyan N20m dan rage musu zafin asarar da suka yi.

Mista Yakadi, yace rundunar ‘yansadan jihar Neja sun fara binciken mutanen da aka kama dan gano wadanda suka dauki nauyin harin da aka kai wa gwamnan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel