Jam'iyyar APC na da rauni - Gwamna Rochas

Jam'iyyar APC na da rauni - Gwamna Rochas

- Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya fito fili ya bayyana cewar har yanzu jam'iyyar APC ba ta da wani tasiri a yankin 'yan kabilar Igbo

- Gwamna Rochas na wannan kalamai ne yayin tabbatar wa da manema labarai cewar jihar zata gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Yuni

- Okorocha, tun bayan hawansa mulki fiye da shekaru shida, bai gudanar da zaben kananan hukumomi ba

Bayan yin alkawura masu yawa ba tare da cikawa ba, gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya bayyana cewar gwamnatinsa zata gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Yuni na shekarar nan.

Kazalika, Rochas, ya amince cewar jam'iyyar sa ta APC har yanzu bata da tasiri a yankin 'yan kabilar Igbo.

Jam'iyyar APC na da rauni - Gwamna Rochas

Jam'iyyar APC na da rauni - Gwamna Rochas

Okorocha na wannan kalamai ne a filin tashi da saukar jirage na Sam Mbakwe jim kadan bayan dawowar sa daga wata tafiya da ya yi zuwa kasashen ketare.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari a Jos, sun kone gidaje da dukiyoyi

Gwamnan ya bukaci majalisar jihar ta gaggauta yiwa dokar zaben jihar gyaran fuska domin samun damar yin zaben kananan hukumomi a jihar a watan Yuni.

Tun bayan hawansa mulki, fiye da shekaru shida, bai gudanar da zaben kananan hukumomi ba a jihar Imo ba.

Saidai, Okorocha, ya ci alwashin karawa jam'iyyar APC karfi a yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo tare da kara jaddada goyon bayansa ga takarar shugaba Buhari.

Rochas ya kara nanata cewar babu gudu babu ja da baya a batun tsayar da surukinsa kuma shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Uche Nwosu, a matsayin dan takarar gwamna jihar Imo.

Okorocha ya kalubanci duk ma su sukar tsayar da surukinsa da su tsayar da nasu dan takarar, sai jama'a su zama alkalai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel