Jam’iyyar PDP ta caccaki Shugaban kasa na rashin amincewa da kudirin ‘yan Majalisa

Jam’iyyar PDP ta caccaki Shugaban kasa na rashin amincewa da kudirin ‘yan Majalisa

- Jam’iyyar adawa ta PDP tayi tir da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya

- PDP ta yi magana game da kin amincewa da kudirin yi wa tsarin zabe gyara

- Shugaban kasar ya ki sa hannun sa a kudiri wanda yace an shiga hakkin INEC

Mun samu labari daga Jaridar Premium Times cewa babbar Jam’iyyar adawa ta PDP tayi ca a kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kin amincewa da kudirin da zai canza tsarin gabatar da zabe a kasar a shekarar 2019.

Jam’iyyar PDP ta caccaki Shugaban kasa na rashin amincewa da kudirin ‘yan Majalisa

Buhari ya ki amincewa da kudirin yi wa yanayin zabe garambawul

Jam’iyyar PDP ta fitar da jawabi ta bakin Sakataren ta ba yada labarai na kasa Kola Olobodiyan inda yace sun yi amanna cewa Majalisa ta na da karfi da hurumi a dokar kasa da za ta sauya tsarin gudanar da zabe a kasar.

KU KARANTA: Za a maka Gwamnatin Shugaba Buhari a Kotu nan da 'yan kwanaki

Shi dai Shugaban kasar bai amince da wannan kudiri ba don haka ya ki sa hannun sa a kan kudirin duk da Majalisu sun yi na’am da shi inda yake cewa wannan yunkuri zai zama an yi waHukumar zabe na INEC katsalandan.

Jam’iyyar adawar tace sam ba tayi mamakin rashin amincewa da wannan kudirin na ‘yan Majalisar da Shugaban kasar yayi ba sai dai Jam’iyyar tace ba ta jin wani tsoro don kuwa ta san cewa Jama’a ba za su zabi APC a badi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel