Ina iya kokari na wajen ganin matasa sun samu aikin yi - Buhari

Ina iya kokari na wajen ganin matasa sun samu aikin yi - Buhari

- Shugaba Buhar ya ce gwamnatin sa tana kokarin samar wa matasan kasar aikin yi

- Buhari ya ce yana matukar farinciki akan yadda matasan Najeriya suka rungumi harkar noma

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yace gwamnatin sa tana iya kokarin ta wajen ganin ta samar wa matasa aikin yi

Da yake jawabi a fadar shugaban kasa a lokacin da Ministan harkan kasashen waje na kasar Tunisia ya kawo mi shi ziyara, shugaba Buhari yace gwamnatin sa ta mayar da hankalin ta wajen inganta harkar noma a kasar.

Ina iya kokari na wajen ganin matasa sun samu aikin yi - Buhari

Ina iya kokari na wajen ganin matasa sun samu aikin yi - Buhari

Babban hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari a fannin watsa labarai, Malam Garba Shehu, bayyana haka a ranar Talata, inda ya ce shugaba Buhari yayi alkawarin inganta fannin noma dan samar wa matasar kasar aikin yi.

KU KARANTA : Shugaban kwamitin shirin ciyar da daliban makaranta Frimare na kasa, ya gargadi malamai akan cinye wa dalibai abincin su

“Ganin yadda kasuwar mai ya fara zuwa kasa, kuma gashi rashin aikin yi yana karuwa a kasar, shiyasa gwamnatin ta karkatar da akalar ta zuwa harkar noma, kuma ina matukar farin ciki da matasan mu suka fara rungumar noma a yanzu,” Inji Buhari.

Ministan harkan kasar waje na kasar Tunisia, Mista Remilli, wanda ya jagoranci tawagar ‘yan kasauwar kasar Tunisia zuwa Najeriya ya fadawa shugaba Buhari cewa a shirye suke su kula sabuwar alaka na kasuwnci da Najeriya ba.

Bayan haka, Mitsa Remilli, ya yabawa shugaba Buhari akan kokarin da yayi a fannin tsaro da kuma inganta tattalin arzikin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel