Dapchi: An shawarci gwamnati ta rufe makarantun kwana a Arewa maso gabashin Najeriya

Dapchi: An shawarci gwamnati ta rufe makarantun kwana a Arewa maso gabashin Najeriya

Biyo bayan mummunan al'amarin da ya auku a satin da ya gabata inda aka ruwaito wasu mahara da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai a makarantar 'yan mata ta kwana dake a garin Dapchi, jihar Yobe inda kuma har aka sace wasu matan masu yawa, an shawarci gwamnatoci da su rufe makarantun kwana.

Wannan dai mun samu daga wani bawan Allah dake rajin tabbatar da adalci da kuma tabbatacen zaman lafiya mai suna Malam Alfaruk wanda ya bayar da wannan shawarar a shafin sa na dandalin sada zumunta na Facebook.

Dapchi: An shawarci gwamnati ta rufe makarantun kwana a Arewa maso gabashin Najeriya

Dapchi: An shawarci gwamnati ta rufe makarantun kwana a Arewa maso gabashin Najeriya

KU KARANTA: Abubuwa 7 da suka faru da Buhari bai sani ba

Legit.ng ta samu cewa, a cewar sa, Alfaruk ya bayyana cewa tun da dai ba wannan ne karo na farko ba da ake kai hari a makarantun kwanan, kuma yanzu ta tabbata cewa jami'an tsaron kasar ba su iya tsare daliban, to abun da yafi kamata shine a rufe makarantun har sai komai ya daidai ta.

A wani labarin kuma, Hukumar nan dake da alhakin shirya jarabawar kammala makarantar Sakandare ta yammacin Afrika watau West African Examination Council, WAEC a jiya ta sanar da fara fitar da sakamakon jarabawar da ta gudanar ga dalibai a cikin farkon shekarar nan ta 2018.

Da yake sanar da hakan a babbar hedikwatar hukumar dake garin Legas, shugaban hukumar Mr. Isaac Adenipekun ya bayyana cewa cikin dalibai 11,307 da suka zauna jarabawar, akalla mutane 1,937 ne kacal suka samu nasarar lashe darussa 5 zuwa sama da suka hada da Turanci da kuma Lissafi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel