'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyin su game da taron gangamin jam'iyyar PDP a Jigawa

'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyin su game da taron gangamin jam'iyyar PDP a Jigawa

A farkon satin nan ne dai, ranar Litinin, 12 ga watan Maris din nan da muke ciki ne dai jam'iyyar adawa ta PDP ta gudanar da babban taron ta na gangamin motsa jam'iyyar a jihar Jigawa dake a arewa maso yammacin Najeriya.

A wajen taron, kusan dukkan masu fada a ji na jam'iyyar a mataki na kasa da kuma jahohin kasar nan sun hallara kuma taron yayi armashi sosai.

'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyin su game da taron gangamin jam'iyyar PDP a Jigawa

'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyin su game da taron gangamin jam'iyyar PDP a Jigawa

KU KARANTA: Batutuwa 7 da suka faru Shugaba Buhari bai sani ba

Ga dai wasu muhimman ra'ayoyin 'yan Najeriya da muka tattaro game da taron:

Jibril Khalil Jibraan ya rubuta cewa: "Tabbas gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo ya ciri tuta kuma idan har aka bashi dama ya mulki Najeriya to ko shakka babu zai iya bakin kokarin su. Haka ma kuma zaman sa matashi zai taimaka sosai."

Onorakpene Eviosekwofa ya rubuta cewa: "Gangami irin wannan ya kamata a ce an gudanar da shi a dukkan jahohin da ke hannun jam'iyyar don kuwa ko ba komai hakan zai zama tamkar tauna tsakuwa ce don aya ta ji tsoro."

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel