Fatali da umurni: Matasan Arewa sun roki Buhari kar ya kori Sifeto janar na 'yan sanda

Fatali da umurni: Matasan Arewa sun roki Buhari kar ya kori Sifeto janar na 'yan sanda

Wasu matasa daga arewacin Najeriya a karkashin inuwar kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) sun fitar da sanarwa inda suka zargi gwamnan jihar Benue da ma wasu da suka kira makiyan Najeriya da shirya kutungwilar tsige babban Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris.

Kungiyar ta tuntuba ta matasan arewacin Najeriya din ta bayyana hakan ne a ta bakin shugaban ta Malam Shettima Yerima wanda ya kuma roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dubi girman Allah da Annabi ya kyale shi kar ya kore shi.

Fatali da umurni: Matasan Arewa sun roki Buhari kar ya kori Sifeto janar na 'yan sanda

Fatali da umurni: Matasan Arewa sun roki Buhari kar ya kori Sifeto janar na 'yan sanda

KU KARANTA: Hukumar jarabawar WAEC ta fitar da sakamakon 2018

Legit.ng ta samu cewa a cikin sanarwar da kungiyar ta fitar, ta bayyana cewa duk da dai cewa shugaban 'yan sandan bai kwana ba a garin Makurdi, babban birnin jihar, amma ya dade sosai a dukkan kananan hukumomi uku da rikicin manoma da makiyaya yafi kamari.

A wani labarin kuma, Shugabannin jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) sun tabbatar wa da 'yan Najeriya cewar jam'iyyar za ta gudanar da zabukan fitar da 'yan takarar shugaban kasa na 2019 cikin gaskiya da kuma mafi kyaun tsaftar yanayi.

Haka ma dai jam'iyyar ta soki shugaban kasar bisa ga kin amincewa da kudurin dokar sauya tsarin jadawalin zabe mai zuwa wanda a cewar su hakan na nuni ne karara da cewa shugaban da kuma jam'iyyar sa sun tsorata ne.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel