Sakacin mulki: Muhimman batutuwa 7 da suka faru da shugaba Buhari bai sani ba

Sakacin mulki: Muhimman batutuwa 7 da suka faru da shugaba Buhari bai sani ba

Reno Omokri, wanda ke zaman tsohon mai taimakawa tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan kar harkokin yada labarai a jiya ya lissafa akalla batutuwa da kuma lokuta bakwai da shugaba Buhari ya nuna bai san me ke faruwa ba a Najeriya da kuma kasashen waje.

Ga dai batutuwan da ya lissafa nan kamar yadda muka samu:

1. Shugaban kasar yace bai san Sifeto Janar na 'yan sanda ya bijire ma umurnin sa ba na yin tafiyar sa bayan ya umurci ya koma jihar Benue da zama.

Sakacin mulki: Muhimman batutuwa 7 da suka faru da shugaba Buhari bai sani ba

Sakacin mulki: Muhimman batutuwa 7 da suka faru da shugaba Buhari bai sani ba

KU KARANTA: Yadda ta kaya tsakanin EFCC da Ali Modu Sheriff

2. Shugaba Buhari din bai san cewa kasar Ghana ta fi saukin cin hanci da rashawa ba.

3. Shugaban ya taba manta cewa ba sunan mataimakin sa Osinbande ba a yayin lokacin yakin neman zaben 2015.

4. Shugaba Buhari bai san cewa yanzu ba bu wani yanki ko kasa mai cin gashin kanta ba da ke da suna Jamus ta yamma.

5. Shugaba Buhari har yanzu bai gano wadanda suka yi aringizo a kasafin kudin shekarar 2016 da kuma 2017 ba.

6. Shugaba Buhari har yanzu bai gano takamaimai wanda ya maida Abdurrashid Maina aiki ba ya kuma yi masa karin girma.

7. Shugaba Buhari bai san cewa yanzu matar sa aikin ta ba na shiga daki bane kawai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel