Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta zayyana yadda za ta fiddo dan takarar da zai kara da Buhari

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta zayyana yadda za ta fiddo dan takarar da zai kara da Buhari

Shugabannin jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) sun tabbatar wa da 'yan Najeriya cewar jam'iyyar za ta gudanar da zabukan fitar da 'yan takarar shugaban kasa na 2019 cikin gaskiya da kuma mafi kyaun tsaftar yanayi.

Haka ma dai jam'iyyar ta soki shugaban kasar bisa ga kin amincewa da kudurin dokar sauya tsarin jadawalin zabe mai zuwa wanda a cewar su hakan na nuni ne karara da cewa shugaban da kuma jam'iyyar sa sun tsorata ne.

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta zayyana yadda za ta fiddo dan takarar da zai kara da Buhari

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta zayyana yadda za ta fiddo dan takarar da zai kara da Buhari

KU KARANTA: Baccin rana na da lahani ga kwakwalwa

Legit.ng ta samu cewa wannan kalaman dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun jam'iyyar Kola Ologbondiyan ya fitar a jiyan inda ya kuma bayyana cewa sun basu jin tsoron zabe.

A wani labarin kuma, Wasu matasa daga arewacin Najeriya a karkashin inuwar kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) sun fitar da sanarwa inda suka zargi gwamnan jihar Benue da ma wasu da suka kira makiyan Najeriya da shirya kutungwilar tsige babban Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris.

Kungiyar ta tuntuba ta matasan arewacin Najeriya din ta bayyana hakan ne a ta bakin shugaban ta Malam Shettima Yerima wanda ya kuma roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dubi girman Allah da Annabi ya kyale shi kar ya kore shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel