Tattalin arziki: Abubuwan da mu ka yi cikin watanni 10 – Buhari

Tattalin arziki: Abubuwan da mu ka yi cikin watanni 10 – Buhari

- Shugaban kasa Buhari ya bayyana nasarorin da Gwamnatin sa ta samu

- Shugaba Muhammadu Buhari yace a fannin tattalin arziki sun yi kokari

- A baya Najeriya ta samu durkushewar tattalin arziki a Gwamnatin nan

Shugaba Buhari ya bayyana irin nasororin da ya samu a harkar tattalin arziki daga bara zuwa yanzu. Shugaban kasar ya bayyana wannan ne lokacin da yake kaddamar da kayan shirin tsarin da ya kawo na farfado da tattalin arzikin kasar.

Tattalin arziki: Abubuwan da mu ka yi cikin watanni 10 – Buhari

Shugaban kasa Buhari yace sun babbako da tattalin arziki

Shugaban kasar ya bayyana yadda tattalin Najeriya ya motsa gaba a 2017 sannan kuma yace an samu daidaito a game da tashin Dalar Amurka. Bugu-da-kari, Shugaban kasar yace kudin kasar wajen Najeriya ya karu daga Dala Biliyan 24 zuwa 46.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da Sufetan 'Yan Sanda jiya

Shugaban Najeriyar yace an samu wannan nasara ne kusan saboda tashin kudin danyen mai a Duniya. A jawabin na sa tunawa jama’a yadda Najeriya ta shiga cikin sahun kasashe 10 da tattalin arzikin su ya gyaru a bara inji babban bankin Duniya.

Bayan nan kuma Shugaban kasar yace Gwamnatin sa na bakin kokari na gina abubuwa more rayuwa a kasar ban da kuma irin nasororin da aka samu a fannin gona musamman a harkar noman shinkafa inda yace yana ma sa rai abubuwa za su kara kyau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel