Canja jadawalin zaben 2019: An fara kulle-kullen yadda za a bullowa Buhari a majalisun tarayya

Canja jadawalin zaben 2019: An fara kulle-kullen yadda za a bullowa Buhari a majalisun tarayya

- 'Yan majalisar wakilai da na dattijai sun bukaci a canja jadawalin zaben shekarar 2019

- A jiya ne shugaba Buhari ya yi watsi da kudirin bayan majalisar ta miko kudirin gaban da domin neman sahalewar sa

- 'Yan majalisun sun fara tuntubar junansu domin kulla yadda zasu bullowa Buhari a kan wannan al'amari

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da kudirin nan da majalisun kasar nan su ka mika ma sa domin neman sahalewar sa a kan canja jadawalin zaben shekarar 2019.

Kamar yadda shugabannin majalisun kasar nan su ka karanta wasikar da Buhari ya aike ma su a jiya, shugaban ya ce daga cikin dalilan da ya sa bai aminta da kudirin ba akwai batun yin katsalandan a kan iko da karfin hukumar zabe ta INEC ke da shi kamar yadda kundin tsarin mulki ya tabbatar.

Canja jadawalin zaben 2019: An fara kulle-kullen yadda za a bullowa Buhari a majalisun tarayya

Canja jadawalin zaben 2019: An fara kulle-kullen yadda za a bullowa Buhari a majalisun tarayya

Tuni dai kayuwa a majalisar dattijai sun rabu tsakanin mambobin majalisar ma su biyayya ga shugaba Buhari da ma su biyayya ga shugaban majalisa Bukola Saraki.

KU KARANTA: Sauya sheka: Mutane fiye da 2000 sun bar APC zuwa PDP a jihar Kano

Shugaba da 'yan majalisar wakilai ba su furta komai ba ya zuwa yanzu, saidai wani bincike da jaridar Punch ta gudanar ya nuna cewar 'yan majalisar dattijai da na wakilan sun fara tuntubar juna domin daukan mataki na gaba.

Wani dan majalisar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, "Shugaban kasa ya yi abinda zai iya, saidai hakan ba yana nufin maganar ta mutu ba kenan, mu ma a namu bangaren akwai abinda zamu iya yi a kan batun."

Shugaban kwamitin watsa labarai da hulda da jama'a a majalisar wakilai, Abdulrazaq Namdas, ya ce za su yi amfani da karfin ikon su idan shugaba Buhari ya ki amincewa da kudirin na su.

A wata tattaunawa da shugaban majalisar dattijai ya yi da Sanatoci, ya ce, za su mika takardar kin amincewar Buhari ga sashen shari'a na majalisar domin neman shawara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel