Abin takaici: Uba ya lalata rayuwar diyarsa mai shekaru 4 ta hanyar aikata mata aika aika

Abin takaici: Uba ya lalata rayuwar diyarsa mai shekaru 4 ta hanyar aikata mata aika aika

Wani kafinta mai shekaru 29, Taiwo Opasina ya gurfana gaban babbar kotun majistri dake Ebute Meta na jihar Legas, inda ake tuhumarsa da laifin zakke ma diyarsa mai shekaru 4, ini rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ana ruhumar Taiwo ne da laifin cin zarafi, fyade da kuma zakke ma karamar yarinya, sai dai ya musanta dukkanin tuhume tuhumen.

KU KARANTA: Rahama sadau ta samu lambar karramawa na ‘Tauraruwa mai haskawa’ daga majlisar dinkin Duniya UN

Dansanda mai shigar da kara, Sufeta Chinalu Uwadione ya bayyana ma Kotu cewa Taiwo ya tafka diyarsa wannan aika aika ne a watan Disamba na shekarar 2017 a gida mai lamba 17 dake titin Magbaola, a unguwar Ajah na jihar Legas.

Dansandan ya shaia ma Kotu cewar ba sau daya ba, ba sau biyu ba, mahaifin yarinyar da aka boye sunanta ya sha sanya yatsunsa tare da al’aurarsa cikin al’aurar diyar tasa.

“Malamar yarinyar ce ta fara lura da wasu sabbin halayen yarinyar, inda take yawan kadace kadanta, bata shiga cikin sauran daliban ajin, kuma sai ta kwashe tswon lokaci ita kadai tana zaune ba uhm, ba uhm uhum”

Dansandan yace wannan laifi da ake tuhumar mahaifin yarinyar ya ci karo da sashi na 135, 137 da 261 na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Legas, sai dai mahaifin ya musanta zarge zargen gaba daya.

Daga nan sai Alkali Ipaye Nwchukwu ta dage sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Afrilu, sa’annan ta bada umarnin garkame Taiwo a kurkuku

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel