Buhari ya aika ma babban Sufetan Yansanda sammaci game da rashin cika umarninsa a Benuwe

Buhari ya aika ma babban Sufetan Yansanda sammaci game da rashin cika umarninsa a Benuwe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika ma babban sufetan Yansandan Najeriya, IGP Ibrahim Idris takardar sammaci don ya gurfanar gabansa domin fada masa hujjar rashin cika umarninsa a Benuwe.

A safiyar ranar Talata 14 ga watan Maris ne IG Idris ya yi sammako ofishin shugaba Buhari, inda ya gana da shi, biyo bayan korafin da shuwagabannin jihar Benuwe suka yi dangane da Sufetan bisa rashin cika umarnin Buhari da ya bashi na cewa ya koma jihar Benuwe da zama don shawo kan rikicin manoma da makiyaya.

KU KARANTA: Zan tsaya takarar shugaban kasa muddin Kwankwaso ya ja da baya – Inji Buba Galadima

Manyan garin sun bayyana ma Buhari cewa tabbas Idris ya je garin Benuwe, amma fa ko sa’o’I 24 bai kwashe a jihar ba, daga nan ya wuce jihar Nassarawa, daga nan kuma ya koma Abuja. A nan ne Buhari ya bayyana musu cewar ba shi da masaniya game da wannan batu, amma zai bincika.

Buhari ya aika ma babban Sufetan Yansanda sammaci game da rashin cika umarninsa a Benuwe

Idris

Sai dai da komawarsa fadar shugaban kasa, sai Buhari ya aika ma Idris sammaci, don ya tsatstsage masa bayani game da rashin cika umarnin nasa, inda Sufetan ya masa kiran shugaba Buhari, kuma suka kwashe mintuna 30 suna tattaunawa.

Mashawarcin shugaban kasa game da al’amuran watsa labaru, Garba Shehu ya tabbatar da faruwar hakan, amma bai bayyana ma majiyar Legit.ng abin da Buhari da Idris suka tattauna ba.

Idan za’a tuna dai anyi cacar baki a tsakanin gwamnatin jihar Benuwe da rundunar Yansandan Najeriya, inda kowanne bangare ke ganin lafin kishiyarsa game da lalacewar tsaro a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel