Badakalar NHIS: Shugaban Hukumar ya wanke kan sa a gaban Majalisa

Badakalar NHIS: Shugaban Hukumar ya wanke kan sa a gaban Majalisa

- Majalisa na zargin cewa an zari wasu makudan Biliyoyi daga asusun TSA

- 'Yan Majalisa sun nemi Ministocin kasar da dama su bayyana a gaban su

- Tuni dai Shugaban NHIS Yusuf Usman ya wanke kan sa gaban Majalisar

Za ku ji cewa Majalisar Wakilan Tarayya ta soma binciken wasu kudi har Naira Biliyan da ake zargi an zara daga asusun bai-daya na kasar watau TSA inda har ta kai an kira wasu daga cikin Ministocin Shugaba Buhari su yi bayani.

Badakalar NHIS: Shugaban Hukumar ya wanke kan sa a gaban Majalisa

Shugaban Hukumar NHIS Farfesa Yusuf Usman

Kwamitin harkar lafiya na 'Yan Majalisar Tarayya sun aikawa Ministan kasafin kasar Udo Udoma da kuma Ministar kudi Kemi Adeosun da ma Gwamnan Babban bankin na CBN Godwin Emefiele sammaci game da Hukumar NHIS.

KU KARANTA: Oby Ezekwensili ta hada ‘Yan Majalisar Najeriya da babban aiki

Majalisar ta nemi ayi mata bayanin dalilin da ya sa aka sa Hukumar NHIS cikin ma'aikatun da ke kawowa Gwamnanti kudin shiga. Ana zargin cewa an zari Naira Biliyan 10 na Hukumar NHIS din wanda dai Shugaban ya karyata.

Yusuf wanda Shugaba Buhari ya maida Ofis bayan an dakatar da shi ya wanke kan sa a gaban Majalisar inda ya kore zargin da ke wuyan sa. Kwamitin ta kuma nemi Ministan lafiya Isaac Adewole da babban Akantan kasar Ahmad Idris su bayyana gaban ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel