Okorocha ya bayyana dalilin zaɓin surinkin sa a matsayin Magajin kujerar sa

Okorocha ya bayyana dalilin zaɓin surinkin sa a matsayin Magajin kujerar sa

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, ya yi karin haske dangane da bayyana ra'ayin sa karara wajen zaɓen Surukin sa, Mista Uche Nwosu a matsayin mai cin gajiyar kujerar sa ta gwamna.

Gwamnan ya bayyana hakan a yayin ganawa da mamena labarai jim kadan bayan saukar sa a filin jirgin sama na Sam Mbakwe dake birnin Owerri, inda ya bayyana cewa ya zaɓi Nwosu ne sakamakon cancantar sa ga kujerar gwamnatin jihar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, gwamnan ya bayyana matsayarsa kan zaɓin surinkin sa bayan dawowar sa daga tafiye-tafiye na kashen ketare.

Rochas Okorocha

Rochas Okorocha

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya kuma ruwaito cewa, al'ummar jihar da dama sun soki gwamnan sakamanon zaɓin surikin sa da cewar ya aikata son kai kuma mulki ba gado ba ne.

KARANTA KUMA: Gwamnatin APC ta yiwa ta PDP fintinkau ta fuskar rashawa - Secondus

A yayin haka kuma, Gwamna Okorocha ya bayyana cewa za a gudanar da zaɓen kananan hukumomi na jihar a watan Yuni na wannan shekara, inda ya nemi al'ummar jihar da su zaɓi dan takarar da ya cancanta wajen jagoranci nagari.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwiato cewa, a daren ranar Litinin din da ta gabata ne rayuka 23 suka salwanta a wani sabon harin makiyaya da afku a jihar Filato.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel