Gwamnatin tarayya zata biya kowanne sansani dala $2,500 a matsayin kudin fansar 'yan Najeriya a Libiya

Gwamnatin tarayya zata biya kowanne sansani dala $2,500 a matsayin kudin fansar 'yan Najeriya a Libiya

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewar tana tattaunawa yadda zata ceto 'yan Najeriya daga kasar Libiya tare da tabbatar da cewar sun dawo gida lafiya.

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) hakan yau, Talata.

Ministan ya ce ya gana da Jakadan kasar Libiya a Najeriya mai barin gado, Dakta Attai Alkhoder, wanda ya hayar da tabbacin samun hadin kan gwamnatin kasar.

Ya bayyana cewar gwamnatin tarayya na aiki tukuru domin tabbatar da kubutar 'yan Najeriya daga kasar Libiya tare da tabbatar da sun dawo gida lafiya.

Gwamnatin tarayya zata biya kowanne sansani dala $2,500 a matsayin kudin fansar 'yan Najeriya a Libiya

'Yan Najeriya a Libiya

Onyeama ya bayyana cewar wasu daga cikin sansanin da 'yan Najeriya ke zaune sun dage a kan sai an biya su kudi kafin su saki 'yan Najeriya da su ke rike da su.

DUBA WANNAN: Jami'an NSCDC da na hukumar JAMB sun kama ma su magudin jarrabawa, za a gurfanar da su gaban kotu

"Mun samu daidaita wa da wasu sansanin a kan biyan dalar Amurka biliya $2,500. A wasu wuraren adadin ya fi haka amma kusan mafi yawan sansanin sun amince da karbar adadin kafin sakin 'yan Najeriya," a cewar Onyeama.

Ministan ya ce ba dukkan 'yan Najeriya ke cikin halin ni-'ya-su a kasar ta Libiya ba tare da bayyana cewar wasu na zaune a kasar bisa ka'ida.

Onyeama ya kara da cewar burin Najeriya shine dawo da dukkan 'ya'yanta gida lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel