Shugaba Buhari na tsoron shan kaye - Jam'iyyar UPP

Shugaba Buhari na tsoron shan kaye - Jam'iyyar UPP

- Jam'iyyar UPP tayi ikirarin cewa tsoron shan kaye ne ya sa shugaba Buhari da APC suka ki amincewa a canja jadawalin zaben 2019

- UPP ta ce yan jam'iyyar na APC suna dogaro ne da gogowar nasarar zaben shugaban kasa don yin nasara shi yasa suke son ya zamo na farko

- UPP ta kara da cewa idan ha APC tayi yarda cewa ta yiwa al'umma aikin da zai sa a sake zaben su bai kamata su ki amincewa da kwaskwarimar ba

A yau Talata ne jam'iyyar United Progressives Party (UPP) ta bayyana cewa kin amincewar shugaba Buhari yayi da kwaskwarimar da Majalisar kasa tayi wa jadawalin zaben 2019 ya nuna yana tsoron shan kaye ne.

Shugaba Buhari ne tsoron shan kaye - Jam'iyyar UPP

Shugaba Buhari ne tsoron shan kaye - Jam'iyyar UPP

A wata sanarwa da ta fito ta bakin shugaban jam;iyyar na kasa, Cif Chekwas Okorie, jam'iyyar ta ce idan da za'a amince da kwaskwarimar da majalisar tayi, kowane dan takara zai lashe zabe ne saboda karbuwar sa ga al'umma da kuma manufofin jam'iyyar sa.

KU KARANTA: Gwamna Ahmed ya amince da dokar dakatar da biyan fansho ga tsaffin gwamnoni a jihar Kwara

"Kin amincewarsa da kudirin ya nuna cewa jam'iyyar ta APC tana tsoron shan kaye a babban zaben na 2019, sauran 'yan jam'iyyar APC sun dogara ne da gogowar nasarar sakamakon zaben shugban kasa.

"Idan har shugaba Buhari ta jam'iyyar APC sunyi imani cewa da gaske sunyi wa al'umma aikin da zai sa a sake zaben su, babu dalilin da zai su ki amincewa da kudirin kwaskwarima ga jadawalin zaben da ake sa ran zai karfafa demokradiya," inji UPP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel