Jami'an NSCDC da na hukumar JAMB sun kama ma su magudin jarrabawa, za a gurfanar da su gaban kotu

Jami'an NSCDC da na hukumar JAMB sun kama ma su magudin jarrabawa, za a gurfanar da su gaban kotu

- Hukumar JAMB tare da hadin gwuiwar jami'an tsaro na civil defence (NSCDC) sun yi nasarar kama wasu da laifin aikata magudi

- Hukumar JAMB ta bayyana cewar an yi nasarar kama ma su aikata magudin ne ta hanyar amfani da na'urorin tsegumi dake aika sako shelkwatar hukumar ta kasa

- Za a gurfanar da wadanda aka kama gaban kotu domin girbar abinda su ka shuka da kuma koyar da darasi ga ma su irin halayyar

Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC tare da ma'aikatan hukumar JAMB sun yi bajakolin ma su aikata magudi a jarrabawar UTME da ake rubutawa.

Kwamandan hukumar NSCDC, Patrick Ukpen, ya gabatar da ma su laifin yau a Abuja.

Ya bayyana cewar biyu daga cikin mutanen uku an kama su ne a makarantar Baptist Academy dake Karu a Abuja.

Ya kara da cewa, daya daga cikin ma su laifin an kama ta ne saboda shiga dakin jarrabawa da wayar hannu ta hanyar boye ta a dan kamfai.

Jami'an NSCDC da na hukumar JAMB sun kama ma su magudin jarrabawa, za a gurfanar da su gaban kotu

Jami'an NSCDC da na hukumar JAMB sun kama ma su magudin jarrabawa, za a gurfanar da su gaban kotu

"Mu na tsare da mutane uku da aka samu da laifin aikata magudi a jarrabawar UTME da ake rubutawa, kuma sun aikata laifuka kamar haka: Wata mai suna Joy Akpabio, ta shiga dakin jarrabawa da wayar hannu, laifin da ya saba da dokokin hukumar JAMB," a cewar kwamandan.

Ya cigaba da cewa, "Bayan mun yi ma ta tambayoyi, mun gano abokin aikata laifinta, Andrew, kuma shi ma mun dakumo Shi."

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya cire shugaban hukumar tsarin yin afuwa na tarayya, ya maye gurbinsa

Kazalika, kwamanda Ukpen ya ce sun yi nasarar kama wani mai suna Mista Egwuonwu, saboda laifin karbar N1,000 daga hannun daliban dake rubuta jarrabawar ba tare da wani dalili ba.

Hukumar JAMB ta gargadi ma su rubuta jarrabawar a kan yin duk wani nau'i na magudin jarrabawa domin, a cewar ta, ta na ganin dukkan abinda ke faruwa a dakunan jarrabawar UTME dake fadin kasar nan ta hanyar amfani da na'urorin tsegumi dake aike da faifan bidiyo.

Hukumar ta ce zata gurfanar da wadanda aka kama gaban kotu domin su karbi bakuncin da zai zama darasi ga ragowar ma su hali irin na su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel