Babban dalilin da yasa gwamnan jigawa ya sa Yansanda su kamo masa wani ɗan jarida

Babban dalilin da yasa gwamnan jigawa ya sa Yansanda su kamo masa wani ɗan jarida

Hujjoji kwarara sun bayyana game da dalilin da ya sanya jami’an rundunar Yansandan Najeriya suka diran ma wani dan jarida a farfajiyar majalisar dokokin kasar nan, inda suka yi awon gaba da shi.

Babban editan kamfanin jaridar Daily Trust, Mannir Dan Ali ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata 13 ga watan Maris, inda yace suna zargin gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru ne ya bada wannan umarnin.

KU KARANTA: Gobara ta lakume rayukan mutane 3 a jihar Kano, 2 na cikin halin rai fakwai mutu fakwai

Dan Ali yace kama dan jaridan mai suna Musa Kirishi baya rasa nasaba da wata talla da jaridar ta buga a shafukanta a ranar 26 ga watan Janairu dake dauke da hotunan Badaru da Obasanjo,

Babban dalilin da yasa gwamnan jigawa ya sa Yansanda su kamo masa wani ɗan jarida

Kirishi

wanda wasu kungiyoyin magoya bayan Abubakar Badaru suka dauki nauyi.

Legit.ng ta ruwaito Dan Ali yana fadin buga tallar keda wuya sai wasu lauyoyin gwamna Badaru suka nesanta gwamnan da wannan tallar, inda suka nemi kamfanin ta watsar da ita, sai kuma a ranar 28 ga watan Janairu Daily Trust ta nesanta kanta daga wannan talla, a ranar 5 na watan Feburairu kuma kamfanin ta nemi afuwan gwamnan.

Amma kwatsam sai Daily Trust ta samu takarda daga rundunar Yansanda jihar Kano wai tana binciken lamarin, tare da sammaci daga kotun babban Alkalin majistri na jihar Kano, hakan ta sa muka baiwa yansandan duk bayanan da suke bukata dangane da binciken da suke gudanarwa.

Sai dai bayan da tirka tirkan ta fara daukan sabon salo, sai Daily Trust ta kai kokenta ga babban sufetan Yansandan Najeriya a ranar 15 ga watan Feburairu, inda Sufetan ya kaddamar da kwamitin bincike, amma abin takaici sai ga shi a yau Yansanda sun kama ma’aikacin mu, sun tafi da shi zuwa Jigawa.

Daga karshe sanarwar ta bukaci a sako dan jarida Musa Abdullahi Kirishi, sa’annan ta bukaci takardar afuwa daga hukumar yansandan jihar Kano, haka zalika kamfanin Daily Trust ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sufetan Yansanda da su tilasta ma Yansandan jihar Kano dawo da Musa Kirishi baskin aikinsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel