Gwamna Ahmed ya amince da dokar dakatar da biyan fansho ga tsaffin gwamnoni a jihar Kwara

Gwamna Ahmed ya amince da dokar dakatar da biyan fansho ga tsaffin gwamnoni a jihar Kwara

- An kafa dokar dakatar da biyan tsaffin gwamnoni da mataimakan su karbar fansho a jihar Kwara

- A kwanakin baya majalisar jihar ta amince da kudirin dokar yanzu kuma gwamna ya rattaba hannu kan dokar don ta fara aiki

- Bayan kafa dokar za'a dakatar da biyan fansho da kuma duk wani allawus ga tsaffin gwamnonin jihar ta mataimakan su

Jihar Kwara ta dakatar da biyan fansho ga tsaffin gwamnoni da mataimakan su

Jihar Kwara ta dakatar da biyan fansho ga tsaffin gwamnoni da mataimakan su

Gwamna Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara ya rattaba hannu kan kudirin yiwa kundin tsarin jihar kwaskwarima don dakatar da biyan kudaden fansho da sauran alawus ga tsaffin gwamnoni da mataimakan su a jihar.

KU KARANTA: Kisan Benuwe: Abubuwa 10 da gwamna Ortom ya fada wa Buhari yayin ziyarar sa

Kamfanin dillanci labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa majalisar jihar a kwanakin baya ta amince ta kudirin na dakatar da biyan kudaden fansho ga tsaffin gwamnoni da mataimakan su.

Kudirin ya biyo bayan sakamakon wata rahoto ne da shugaban kwamitin ayyukan al'umma na majalisar jihar, Emmanuel Abodurin ya gabatar da gaban majalisar.

Yanzu da gwamnan Jihar ya sanya hannu kan kudirin dokar, tsafin gwamnoni da mataimakan su za su dena karbar kudaden fansho da wasu allawus da suke karba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel