Yaki da rashawa: Sai Buhari ya damke Obasanjo za mu san dagaske yake - Kalu

Yaki da rashawa: Sai Buhari ya damke Obasanjo za mu san dagaske yake - Kalu

Wani jigo na jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya damki tare da gurfanar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo domin ya tabbatar da gaskiyar sa kan yaki da rashawa.

Tsohon gwamnan ya kalubalanci shugaba Buhari a yayin wani taro da aka gudanar a babban birnin tarayya mai taken tsarin gudanar da shugabanci nagari.

Shugaba Buhari

Shugaba Buhari

Yake cewa, al'ummar Najeriya ba za su tabbatar da muhimmanci tare da tsananin yaki da cin hanci da rashawa da Buhari ya sanya a gaba face ya damko tsohon shugaban kasa Obasanjo bisa laifukan kudaden wutar lantarki da suka yi layar zana a lokacin gwamnatin sa.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Kasar Mauritania ta mayar da N92, 520 a matsayin sabon mafi karancin albashi

Kalu ya ci gaba da cewa, muddin shugaba Buhari bai aikata hakan ba to kuwa ba bu wani yakar rashawa da ake yi a kasar nan, inda ya hikaito dalar Amurka miliyan 16 da ta yi tsuntsunwa a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasar.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a daren ranar Litinin din da ta gabata kimanin rayuka sama da 20 ne suka salwanta a wani sabon harin makiyaya da ya afku a jihar Filato.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel