Gobara ta lakume rayukan mutane 3 a jihar Kano, 2 na cikin halin rai fakwai mutu fakwai

Gobara ta lakume rayukan mutane 3 a jihar Kano, 2 na cikin halin rai fakwai mutu fakwai

Jami’an kwana kwana sun ceto wasu kananan yara guda biyar tare da wani babba guda daya daga cikin wani gidan da wata mummunar gobara ta tashi a ciki, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN ta ruwaito.

Kaakakin hukumar kwana kwana ta jihar Kano, Saidu Mohammed ne ya tabbatar da haka a ranar Talata 13 ga watan Maris, inda yace daga cikin wadanda jami’an hukumar suka ceto akwai karamin yaro mai shekaru 2.

KU KARANTA: Rahama sadau ta samu lambar karramawa na ‘Tauraruwa mai haskawa’ daga majlisar dinkin Duniya UN

Malam Saidu yace gobarar ta taso ne a sakamakon wutar na’urar dafa abinci na iskar gas a gidan dake Layin gado-da-masu, dake cikin unguwar Dorayi na jihar Kano, inda yace wani makwabcinsu Musa Haruna ne ya kira yan kwana kwana da misalin karge 6:06 na yammacin ranar Litinin 12 ga watan Maris.

Gobara ta lakume rayukan mutane 3 a jihar Kano, 2 na cikin halin rai fakwai mutu fakwai

Gobara

Kaakakin ya bayyana sunayen mutanen kamar haka: Usman Ibrahim, mai shekaru 2; Rukkaiya Umar mai shekaru 5; Baffa Umar mai shekaru 8; Al-Amin Ibrahim mai shekaru 10, da kuma Zainab Mohammed, 35.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakkain yana fadin cewa daga cikin mutum biyar da suka ceto, guda uku sun rigamu gidan gaskiya a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, yayin da sauran gida biyu ke cikin halin rai fakwai mutu fakwai a Asibitin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel