Karkatar da N10m: EFCC ta damke wani mutum 'dan damfarar yanar gizo

Karkatar da N10m: EFCC ta damke wani mutum 'dan damfarar yanar gizo

- Hukumar EFCC ta gurfanar da wani Ogungbile Oluwaseun gaban babban kotun da ke Ikeja a Legas

- Ana tuhumar da kutse cikin bayyanan sirrin wani kamfani inda ya yi amfani da bayyanan wajen karkatar da N10m zuwa asusun ajiyar sa

- Wanda ake tuhuma ya musanta aikata laifin kuma kotu da ce a cigaba da tsare shi kafin ranar da za'a fara sauraron shari'ar

Hukumar Yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC, reshen jihar Legas ta gurfanar da wani da ake zargi dan damfarar yanar gizo ne, Ogungbile Oluwaseun gaban mai shari'ah O.A. Williams na babban kotun Ikeja bisa laifin kutse cikin bayyanan sirri na wani kamfani da kuma karkatar da kudi naira miliyan goma.

Karkatar da kudi N10m: EFCC ta damke wani mutum 'dan damfarar yanar gizo

Karkatar da kudi N10m: EFCC ta damke wani mutum 'dan damfarar yanar gizo

Ana tuhumar sa ne da damfarar wani kamfani mai suna Cenoux Express Limited inda yayi kutse cikin bayyanan sirrin kamfanin ta hanyar amfani da yanar gizo, ya kuma yi amfani da bayanan da ya samu wajen karkatar da kud N10m daga Bankin Guaranty Trust zuwa asusun ajiyar sa.

KU KARANTA: Sanata Abdullahi ya janyo hankalin abokan aikin sa kan yiwa gwamnatin Buhari zagon kasa

Kamar yadda mai shigar da kara ya bayyana, wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 19th ga watan Afrilun 2012 kuma ya ce laifin ya sabawa sashi na 385 na dokar masu laifi na jihar Legas na 2011.

Bayan karanto masa zargin, wanda ake tuhuma ya musanta aikata laifin, Lauyan wanda suka shigar da kara, Nkereuwem Anana, ya roki kotu ta bayar da umurnin tsare wanda ake tuhuma a gidan yari har zuwa rannan da za'a fara sauraron kara.

Lauya mai kare wanda ake tuhuma, J.J. Isijola ya sanar da kotu niyyar sa na neman belli, kuma ya nemi alfarma kotu ta tsayar da ranar sauraron karar cikin kankanin lokaci.

Alkalin Kotu, Mai shari'ah Williams ya daga sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Maris inda ya kuma umurci EFCC ta cigaba da tsare wanda ake tuhuma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel