Shugaba Buhari ya bayyana dalilin watsi da dokar sauya fasalin zabe

Shugaba Buhari ya bayyana dalilin watsi da dokar sauya fasalin zabe

Da sanadin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu ya yi fatali da dokar sauya fasalin gudanar da zabe, inda ya aika da rubutacciyar wasika zuwa ga shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki tare da bayyana dalilan sa na aikata hakan.

Shugaba Buhari

Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya aikawa da shugaban majalisar wasika ta bayyana dalilan sa na yin fatali da dokar majalisar ta sauya fasalin gudanar da zaben 2019 bayan da hukumar zabe ta riga da fitar wa tun karshen shekarar da ta gabata.

KARANTA KUMA: Bayan shekaru 22, za a kafa Jami'ar Jiha ta farko a Zamfara

Legit.ng ta ruwaito cewa, wasikar shugaba Buhari ta bayar da gamsassun dalilai kamar haka:

1. Sauya fasalin zabe dake cikin sashe na 25 dake cikin dokar zai ci karo da sashe na 15 dake cikin kundin tsarin mulki da ya baiwa hukumar zabe dama ta tsarawa tare da gudanar da zabe ba tare da wani ya mata kutse ba.

2. Sauya sashe na 138 cikin dokar zaben da take baiwa 'yan takara dama da kalubalantar sakamakon zabe zai dakile damar da suke da ita wajen gudanar da zaben gaskiya da aminci ba tare da magudi ba.

3. Sauya sashe na 152 cikin sashe na 325 zai janyo tasku cikin kundin tsari tare da dakile damar 'yan majalisar dokokin na tarayya wajen yin ruwa da tsaki a zaben kananan hukumomi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel