Kotu ta yanke ma wasu makiyaya kananan yara guda 5 zaman Kurkuku a jihar Benuwe

Kotu ta yanke ma wasu makiyaya kananan yara guda 5 zaman Kurkuku a jihar Benuwe

Wata Kotun majistri a garin Makurdi na jihar Benuwe sa yane ma wasu makiyaya su 5 hukuncin zaman gidan kaso na tsawon watanni 27 bisa kamasu da laifin miyagun ayyuka da kuma karya dokar hana kiwo a jihar.

Makiyayan suna hada da Yusufu Buhari, 22; Hamidu Mama, 11; Saleh Muhammadu, 22; Ali Ibrahim, 12, da Idi Bature, 11, wanda Alkalin Kotun Emmanuel zembe yace sun amsa laifinsu da kansu, sa’annan ya kara da cewa sun yi ma sashi na 97 da 19 (2) na dokokin hana kiwo karan tsaye.

KU KARANTA: Duniya ina zaki damu ne? Yadda wata Mata ta hallaka wani dan jariri ta jefa gawar cikin masai

Da farkon zaman na ranar Talata 13 ga watan Maris, sai da Dansanda mai shigar da kara Sajan Ato Godwin ya bayyana ma Kotu cewar hukumar tsaro ta farin kaya ce ta kama makiyayan a karkashin jagorancin jami’in hukumae ASC Terna Raphael a ranar 7 ga watan Maris.

Kotu ta yanke ma wasu makiyaya kananan yara guda 5 zaman Kurkuku a jihar Benuwe

Makiyaya

Sajan Ato yace an kama makiyayan ne a lokacin da suka saki dabbobinsu suna barna a gonar rogo na mutanen garin, a wani kauye dake cikin karamar hukumar Guma, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Sai dai lauyan wadanda ake kara, Tijjani Ahmed ya roki kotun da ta sassauta hukuncin, duba da shekarun kananan yaran dake cikinsu, daga nan ne sai Alkalin ya sassauta musu hukunci, inda ya yanke musu hukuncin watanni uku a gidan Yari na aikata miyagun laifi, ko kuma su biya taran kudi N3000.

“Amma game da yi ma dokar hana kiwo karan tsaye kuwa, Kotu ta yanke musu hukuncin zaman gidan yari na watanni 24 ko kuma su biya tarar N30,000 kowannensu.” Inji Alkalin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel