Da dumi-dumi: Trump ya kori sakataren wajen Amurka Rex Tillerson

Da dumi-dumi: Trump ya kori sakataren wajen Amurka Rex Tillerson

Donald Trump, shugaban kasar Amurka, ya sanar da cire sakataren wajen Amurka Rex Tillerson tare da maye gurbinsa da darekta a hukumar CIA, Mike Pompeo.

Shugaban kasar ya tabbatar da hakan a wani sako da watsa a shafinsa na Tuwita da safiyar yau.

"Mista Pompeo, darekta a hukumar leken asiri ta CIA, shine sabon sakataren wajen kasar Amurka. Zai yi aiki mai kyau. Ina godiya ga Rex Tillerson bisa aikin da ya yi mana," a cewar Trump.

Canje-canje a mukaman gwamnatin kasar Amurka na zuwa ne bayan wata ganawar gemu da gemu tsakanin shugaba Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa, Kim Jong-un.

Da dumi-dumi: Trump ya kori sakataren wajen Amurka Rex Tillerson

Rex Tillerson yayin ganawa da Buhari

Tun a juma'ar da ta gabata ne shugaba Trump ya bukaci Tillerson ya koma gefe, dalilin da ya saka shi katse ziyarar kasashen Afrika da ya keyi tare da komawa gida Amurka daga Najeriya, kamar yadda jaridar Telegraph UK ta rawaito.

Sai dai a jiya ofishin jakadancin kasar Amurka dake Najeriya ya bayar da sanarwar cewar Tillerson zai ziyarci Najeriya kuma har ma ya samu ganawa da shugaba Buhari bayan isowar sa.

DUBA WANNAN: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani a kan sakataren wajen Amurka Rex Tillerson

Da yake yabon sabon sakataren wajen kasar ta Amurka, Trump, ya ce, "Mike mutum ne mai kwazo da ya fita da sakamako mafi daraja a makarantar koyon aikin shari'a dake Harvard kafin daga bisani ya hidimtawa kasar Amurka a matsayin soja."

Trump ya kara da cewa, "Mike ya yi aiki a matsayin dan majalisa kuma ya samu yabo bisa irin hazaka da kishin kasa da ya nuna."

Trump ya zabi Gina Haspel a matsayin madadin darekta Pompeo a hukumar CIA saboda dadewar sa da kuma dadewar su ta iki tare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel