Rayuka 23 sun salwanta a wani sabon harin makiyaya a jihar Filato

Rayuka 23 sun salwanta a wani sabon harin makiyaya a jihar Filato

Kimanin rayuka 23 ne suka salwanta a wani sabon harin makiyaya da ya afku a daren ranar Litinin din da ta gabata a kauyen Dundu dake karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Daya daga cikin shugabannin matasa na garin Miango Mista Auta Danjuma, shine ya tabbatar da afkuwar wani hari a daren, inda rayuka 23 wanda mafi akasarin su mata da kananan yara suka salwanta yayin da wasu dama suka raunata.

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong

Jaridar New Telegraph ta ruwaito cewa, wannan shine hari na biyar kenan da afku a jihar cikin makonnin kalilan da suka gabata a tsakanin garuruwan Bokkos da kuma Bassa na jihar.

KARANTA KUMA: Sirrika 10 da Kwallon Kashu ya kunsa ga lafiyar Dan Adam

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, DSP Mathias Terna, ya tabbatar da wannan lamari na harin dare da ya afku, inda ya nemi manema labarai su kara ba shi lokaci na tatso rahotanni kan ibtila'in da ya afku.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnatin kasar Mauritania ta mayar da N92, 520 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel