Da dumimsa: Bayan fiye da shekara guda, Majalisa ta yafe wa Abdulmumin Jibrin

Da dumimsa: Bayan fiye da shekara guda, Majalisa ta yafe wa Abdulmumin Jibrin

Majalisar Wakilai na Tarayya ta dage dakatarwar da tayi wa Abdulmumin Jibrin, dan majalisa mai wakiltar yankin Kiru/Bebeji daga jihar Kano.

Majalisar ta dage dakatarwan ne bayan Mista Jibrin ya rubuta wasika inda ya nemi gafarar majalisar bisa laifin da ya aikata.

Da dumimsa: Bayan fiye da shekara guda, Majalisa ta yafe wa Abdulmumin Jibrin

Da dumimsa: Bayan fiye da shekara guda, Majalisa ta yafe wa Abdulmumin Jibrin

Kakakin majalisar, Yakubu Dogara ne ya karanto wani sashi daga cikin wasikar inda ya fadawa majalisar cewa Abdulmumin ya nemi afuwar Majalisar kuma ya cike dukkan sharruddan da aka gindaya masa.

KU KARANTA: An kama mutane 145 da ake zargi da hannu wurin fadan makiyaya da manoma

"Bayan rubuta wannan wasikar, ya cika dukkan sharruddan da aka gindaya masa kuma yana iya dawowa bakin aikin sa duk lokacin da ya shirya"

An dai dakatar da Mista Jibrin ne a shekarar 2017 na tsawon kwanakin aiki 180 saboda fallasa karin kudade da akayi cikin kasafin kudin shekarar a majalisa.

Sai dai dakatarwar da akayi masa ta dara kwanakin aiki 180 da ake diba masa wanda yayi dai-dai da shekara daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel