Majalisar Tarayya data Wakilai suna zargin junan su akan kasafin kudin 2018

Majalisar Tarayya data Wakilai suna zargin junan su akan kasafin kudin 2018

- A Najeriya dai an kasa kaddamar da kasafin kudin wannan shekarar

- Shugaban kasa ya gabatar da kasafin kudin ga majalisa wata biyar da suka wuce

- Zargi mai karfi ya shiga tsakanin majalisar zartaswa da ta dokoki

Majalisar Tarayya data Wakilai suna zargin junan su akan kasafin kudin 2018

Majalisar Tarayya data Wakilai suna zargin junan su akan kasafin kudin 2018

Zargi mai karfi ya shiga tsakanin sashen majalisar zartaswa dana majalisar dokoki akan gabatar da kasafin kudin wannan shekarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa majalisa kusan watanni biyar da suka wuce.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Tarayya zata yi sulhu da 'yan Boko Haram akan 'yan matan Dapchi

Shugaban hukumar kasafin kudin, Mista Ben Nwabueze ya bawa manema labarai wata takarda dauke da sa hannun sa inda ya ke karyata zargin da majalisar dokoki ta yi na cewa hukumomi da ma'aikatun gwamnati sune su ke bata lokaci wurin bada hadin kai akan gabatar da kasafin kudin.

Mai magana da yawun majalisar dattawa Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce, a lokacin da aka kawo kasafin kudin an riga anyi aiki kusan kashi hamsin, sannan kuma bayan wata uku an kara yin wasu kashi 20 ko 30 mutane zasu gane aikin da aka yi." A cewar sanatan ya ce ba ayi wa masu neman aiki adalci ba, tunda da yawa sun kashe kudin su da dukiyoyin su wurin ganin sun samu ayyukan da aka tallata musu.

'Yan Najeriya suna ta faman korafi akan rashin cika alkawarin da gwamnatin shugaba Buhari ta ke, inda wasu da yawa suke ganin kamar manyan kasar kawai suna yiwa kansu aiki ne, sun manta da cewa jama'a ne suka zabe su domin su yi masu aiki.

Majalisar dattawa ta bawa majalisar zartaswa mako daya ta kammala duk wasu shirye shiryen ta, idan ba haka ba kuma majalisar zata dauki mataki mai karfi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel