Idan kun cika ‘Yan halal, ku fada mana albashin ku – Oby Ezekwensili ta kalubalanci Majalisa

Idan kun cika ‘Yan halal, ku fada mana albashin ku – Oby Ezekwensili ta kalubalanci Majalisa

- An kalubalanci ‘Yan Majalisar Najeriya da su bayyana albashin su

- Babu wanda ya san irin albashin da ‘Yan Majalisar kasar ke dauka

- Kwanaki wani Sanatan Kaduna ya fara fasa kwan da a ba a sani ba

Mun samu labari tsohuwar Ministar ilmi ta Najeriya watau Oby Ezekwensili ta nemi Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da su bayyana albashin su.

Idan kun cika ‘Yan halal, ku fada mana albashin ku – Oby Ezekwensili ta kalubalanci Majalisa

Oby Ezekwensili tayi kira ga Saraki da kuma Dogara

Tsohuwar Ministar ilmi ta kasar ta tsoma bakin ta cikin tattaunawar da ake yi yanzu game da albashin ‘Yan Majalisar Tarayya. Hakan na zuwa ne bayan Sanata Shehu Sani na Kaduna ya fasa kwan abin da ke faruwa a Majalisar Tarayyar kasar.

KU KARANTA: Akwai masu yi wa Buhari zagon-kasa a Majalisa - Sanata

Ministar a lokacin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo tace tun ba yau ta ke neman ‘Yan Majalisa su bayyanawa Duniya abin da su ke karba duk wata ba. Eze tace a lokacin baya, sukar ta Majalisa tayi da ta nemi su bayyana albashin su.

Madam Eze tayi kira ga Shugabannin Majalisar da sauran ‘Ya ‘yan ta da cewa idan ba ga tsoro ba, su kira zama inda Duniya za ta hallara domin ta bayyanawa kowa abin da ake biyan su a kowane wata. Sai dai har yanzu Majalisar tayi tsit.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel