Dalilin da ya sa Buhari bai san Sifeton ‘yan sanda ya bijirewa umarninsa ba – Adesina

Dalilin da ya sa Buhari bai san Sifeton ‘yan sanda ya bijirewa umarninsa ba – Adesina

- Shugaba Buhari ya bayyana mamakinsa bayan da aka sanar da shi cewar babban sifeton ‘yan sanda, Ibrahim Idris, bai yi biyayya ga umarninsa ba

- A jiya ne aka sanar dad a shugaba Buhari cewar babban sifeton ‘yan sanda ya tare a jihar Nasarawa ne bayan shugaba Buhari ya umarce shi ya koma jihar Benuwe

- A karshen shekarar da ta gabata ne, 2017, shugaba Buhari ya umarci Idris ya tattara komatsansa ya koma jihar Benue har sai an kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a jihar

A jiya ne, yayin ziyarar day a kai jihar Benuwe, shugaba Buhari ya bayyana mamakinsa da jin cewar babban sifeton ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, bai yi biyayya ga umarninsa na komawa jihar ba.

A karshen shekarar da ta gabata ne, 2017, shugaba Buhari ya umarci Idris day a tattara komatsansa ya koma jihar Benuwe har sai an kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyi a jihar sakamakon rikicin dake tsakanin makiyaya da manoma.

Dalilin da ya sa Buhari bai san Sifeton ‘yan sanda ya bijirewa umarninsa ba – Adesina

Buhari da Sifeto Ibrahim Idris

Rahotanni sun bayyana cewar Idris ya wuce jihar Nasarawa ne sabanin jihar Benuwe da shugaban kasa ya umarce shi ya koma.

Da yake kare shugaban kasa a kan sukar da ‘yan Najeriya ke yi ma sa bayan ya bayyana cewar bashi da masaniyar Idris ya bijirewa umarninsa, kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, y ace Buhari ba masanin gaibu ba ne, ba allan-musuru ba ne, kuma ba wai ya san komai ba ne duk da kasancewar sa shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Turawan dake satar danyen man fetur a Najeriya sun shiga hannu, duba hotunansu da jiragensu

Adesina na wadannan kalamai ne da safiyar yau, Talata, a wani shirin gidan radiyon Ray Power mai taken “political Flatform”. Kazalika, ya bayyana cewar, duk da ana mikawa shugaban kasa rahotanni kullum, hakan ba yana nufin zai san duk wani abu dake faruwa ba.

Kakakin na shugaba Buhari ya kara da cewar shugaba Buhari ya damu da dukkan mutanen Najeriya kuma ba zai taba yarda da asarar rayukan ko dukiyoyin wata kabila ba.

‘Yan Najeriya na cigaba da sukar Buhari a kan bayyana mamakinsa ga rashin sanin biyayya ga umarninsa da Idris ya yi domin jaridun Najeriya da dama sun kwarmata zancen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel